20 Agusta 2024 - 08:20
Jami'an Tsaron Isra'ila Cikin Damuwa Da Aukuwar Wata Sabuwar Intifada A Gabar Yammacin Kogin Jordan Bayan Harin Tel Aviv

Jaridar ‘Yediot Aharnot’ ta yahudawan sahyuniya ta ruwaito damuwar jami’an tsaro na gwamnatin sahyoniyawa game da faruwar wani sabon intifada a yammacin gabar kogin Jordan tare da daukar matakin yaki da yahudawan sahyoniya a birnin Tel Aviv na baya-bayan nan a matsayin daya daga cikin alamominsa.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta maku bisa nakaltowa daga shafin sadarwa IRNA a yau Talata cewa, jaridar Yediot Aharnot ta yahudawan sahyuniya ta yi ishara da harin da aka kai a daren Lahadin da ta gabata a birnin Tel Aviv, tana mai sanar da cewa: Kafin harin bam a birnin Tel Aviv, sashen leken asiri na soji a matakin soji da na tsaro kan halin da ake ciki a Yammacin Kogin Jordan ya zama mai tsanani har ta kaiga saran aukuwar wani sabon intifada kuma afkuwar hare-haren (neman shahada).

Wannan kafar yada labaran yahudawan sahyoniya ta kara da cewa: Hare-haren da ake kaiwa Tel Aviv na daya daga cikin alamu da dama da ke jaddada cewa ya kamata a dauki mataki game da yiwuwar karuwar hare-haren makamai a yammacin kogin Jordan.

Kafin haka dai kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyawan sun bayar da rahoton cewa, bayan farmakin da makiya sahayoniya suka kai a birnin Tel Aviv, 'yan sanda da kuma kungiyar tsaro ta cikin gidan gwamnatin sahyoniyawan da ake kira Shabak, sun sanar da karuwar matakan faɗakarwa a wannan birni tare da bukatar sahyoniyawan da su yi taka tsantsan.

A halin da ake ciki kuma, Bataliyoyin shahidai na "Izzidin Qassam" reshen soji na kungiyar Hamas da "Sarayal-Quds" reshen soja na kungiyar Jihad Islami sun dauki alhakin kai harin kunar bakin waken a Tel Aviv.

Kungiyar Al-Qassam ta sanar a cikin wannan sanarwa cewa: Muna tabbatar da cewa muddin 'yan mamaya suka ci gaba da kisa da korar fararen hula da kuma ci gaba da manufofin ta'addanci, to ayyukan kunar bakin waken za su koma cikin yankunan da aka mamaye.

Shabak ta tabbatar da cewa fashewar da daddare a Tel Aviv ta masu adawa da Yahudawa ne kuma mai gudanar da aikin ya fito ne daga Nablus, dake gabar yammacin kogin Jordan.

Majiyoyin yada labaran yahudawan sahyuniya sun ruwaito a daren Lahadin da ta gabata cewa, fashewar wani abu a birnin Tel Aviv ya samo asali ne sakamakon wani bam da kuma aikin neman shahada.

A cewar wadannan majiyoyin, mutumin da ya yi shahada yana da belin bam, kuma da alama bam din da wannan mutumin yake dauke da shi ya tashi kafin lokacin da aka tsara.